[Manyan Labarai]: Babu Abunda Zai Samu Sakamakon Zaben Governor Kano >>> INEC - ONLINE NEWS OKZ

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Monday, 11 March 2019

[Manyan Labarai]: Babu Abunda Zai Samu Sakamakon Zaben Governor Kano >>> INEC


Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da cewar sakamakon zaben gwamna a jihar Kano na nan daidai kuma babu abunda zai same shi.

Mutane na cikin halin fargaba kan tsawon lokacin da aka dauka ba a sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa ba dake jihar.
Kwamishinan zabe na jihar Kano, Farfesa Ristuwa Arabu Shehu, ya bayar da tabbacin yayinda yake jawabi ga manema labarai kan rigimar da ke tattare da dogon lokacin da aka dauka wajen hada sakamakon zabenzaben .

Ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta yi adalci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Shehu ya jadadda cewa INEC za ta sake harhada sakamako daga bayanan farko da na biyu inda aka kammala harhada 10 cikin mazabu 11.

1 comment:

  1. Muna Kira da hukumomi da su adalci akan zaben jahar kano.domin dukkan mu yan kano ne bama son tashin hankali ko murdiyar zabe DUK Wanda yaci a bashi kawai,amma ya ake so a Raina mana hankali ne har adinga hadamu rigima da abokan mu.

    ReplyDelete

Featured post

[Kannywood]: Hafsat Idris 'Yar Kwalisa.

                Tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris kenan a wadannan kayatattun hotunan nata data sha kyau, tubarkallah.

Post Top Ad

Responsive Ads Here