[Manyan Labarai]: INEC Tafadi Sunayen Jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar - ONLINE NEWS OKZ

Post Top Ad

Responsive Ads Here

Thursday, 21 March 2019

[Manyan Labarai]: INEC Tafadi Sunayen Jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar


- Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fidda sunayen jihohi 18 da za ta gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar .

- INEC ta ce karashen zaben gwamna zai gudana cikin jihohi biyar na Najeriya .

- Hukumar INEC ta wassafa adadin kananan hukumomi da karashen zaben zai gudana cikin jihohi 18 na Najeriya .

     A ranar Alhamis, 21 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC, ta fidda sunayen jihohi 18 da zaben cike gurbi da kuma karashen zabe zai gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, rahoton da hukumar INEC ta fitar ya bayyana yadda zaben cike gurbi na gwamna zai gudana cikin wasu jihohi 5 da Najeriya ta kunsa.

1. Bauchi (Karamar Hukuma daya)
2. Bayelsa (Kananan Hukumomi uku)
3. Benue (Kananan Hukumomi tara)
4. Ebonyi (Kananan Hukumomi uku)
5. Edo (Karamar Hukuma daya)
6. Ekiti (Karamar Hukuma daya)
7. Kaduna (Karamar Hukuma daya)
8. Adamawa (Kananan Hukumomi biyu)
9. Kano (Karamar Hukuma daya)
10. Kogi (Kananan Hukumomi uku)
11. Imo (Kananan Hukumomi biyar)
12. Lagos (Karamar Hukuma daya))
13. Nasarawa (Kananan Hukumomi hudu)
14. Osun (Karamar Hukuma daya)
15. Plateau (Karamar Hukuma daya)
16. Sokoto (Kananan Hukumomi biyu)
17. Taraba (Kananan Hukumomi biyu)
18. Abuja (Kananan Hukumomi hudu)

No comments:

Post a Comment

Featured post

[Kannywood]: Hafsat Idris 'Yar Kwalisa.

                Tauraruwar fina-finan Hausa, Hafsat Idris kenan a wadannan kayatattun hotunan nata data sha kyau, tubarkallah.

Post Top Ad

Responsive Ads Here