Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR (Khadimul-Islam) na jam'iyyar APC ya lashe zaben gwamna a jihar Kano a wa'adin shugabanci na biyu, kamar yadda hukumar zabe (INEC) ta bayyana ranar Lahadi.
Ganduje ya kayar da Abba Kabir Yusuf dan takarar babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, bayan sanar da sakamakon zaben jihar da aka kammala a ranar Asabar 23 ga watan Maris.
Gwamna Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 35,637 inda jam'iyyarsa ta APC ta samu kuri'a 45,876 yayin da PDP ta samu 10,239.
Yanzu jimilla, APC ta samu kuri'a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713.
Hakan na nufin Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri'a 8,982.

 
 
![[Manyan Labarai]: Maimaita Zaben Kano Kowa ta sa ta fishe shi>>> Shugaba Buhari](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEio1Bc_77z3QMyBlu6YRhnYdgK37lmSuRHk2hkQod4BOuAUhJ82mRIuZaq4X9QT3zhqFnCg6lwrn_SK2P5UxU5ue4Vz9ThaE3FRTMwCiJLAiqbppPrTNlQmcjqhc9IpaePvpUbvz00IuAeJ/s72-c/muhammadubuhari-20190319-0001.jpg) 
No comments:
Post a Comment