Watanni 10 bayan ya bar kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zidane ya sake dawowa a matsayin sabon kociyan kungiyar da zai maye gurbin Santiago Solari, wanda ya jagoranci kungiyar na tsawon watanni 5 kacal.
Zidane, tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid, ya bar kocin kungiyar ne bayan ya kai ta ga nasara a gasar zakarun turai har sau uku a jere.
Mai shekaru 46, Zdane zai cigaba da jan ragamar kungiyar har zuwa shekarar 2022, kamar yadda mahunkuntar kungiyar su ka sanar.
Kungiyar Madrid na mataki na uku a gasar kasar Spain, akwai tazarar maki 12 tsakanin Madrid da Barcelona, babbar abokiyar hamayyar ta da ke mataki na daya.
Kungiyar ta salami Solari duk da nasarar doke kungiyar Valladolid 4-1 a wasan gasar Laliga da su ka fafata ranar Lahadi.
Mahukuntar kungiyar Madrid sun yanke shawarar sallamar Solari ne bayan kungiyar Ajax ta kasar Neitherland ta lallasa ta har gida da 4-1. Kazalika kungiyar ta sha kashi a hannun babbar abokiyar hamayyar ta a fafatawar su a gasar cin kofin Copa del Rey da gasar Laliga da ake yiwa take da El Lasico.
Zidane ya ajiye aikin kocin kungiyar Madrid bayan samun nasarar doke kungiyar Liverpool a wasan karshe na cin kofin gasar zakarun turai.
Solari ya zama kociyan Madrid bayan kungiyar ta salami Julen Lopetegui, wanda ya karbi aiki daga hannun Zidane.
“Real Madrid na mika godiya ga Solari bisa jazircewa da biyayyar sa ga aikin sa, ” a cewar kungiyar.

No comments:
Post a Comment